YADDA AKE HADA KALA- KALAN JUICE
WWW.GIDANAURE.BLOGSPOT.COM""
08107426891
¤ GINGER OF ORANGE JUICE
Kayan hadi : -
•Citta danya
•leman zaki
• suger
• flavour
YADDA AKE HADAWA bare bayan citta wanke idan angama sai a markada a blender, tace ajiye gefe daya .
matse lemo da juice mider idan angama sai a zuba wannan cittar a ciki zuba kankara da flavour .
za ’a sha da sanyi .
¤ GUAVA OF GINGER JUICE
Kayan hadi : -
• Citta danya
•Gova
• Kanunfari
•Leman zaki
• Suger
•Flavour
• YADDA AKE HADAWA
dafa suger da kanunfari tace ajiye gefe daya .
bare bayan citta wanke sai a markada a jiye gefe daya.
markada gova sai a tace ,zuba gova da citta , leman zaki a kwano juya kara suger da flavour zuba kankara.
a sha da sanyi.
¤ MILK SHAKE
Kayan hadi : -
• Oval tine or milo
•Flavor
• Suger
•Madara
YADDA AKE HADAWA
zuba madarar gari a kwano zuba milo ko ovaltine , zuba ruwa sai a kada shi sosai har yayi kumfa ,zuba kankara da suger dai dai bakinka.
zuba a jug .
idan anga ya kwanta sai akara juyashi .
¤ PINEAPPLE AND YOGURT ICE
Kayan hadi : -
• Abarba
• Yoghurt
•Flavor
•Suger
YADDA AKE HADAWA
yanka abarba markada a blender, tace zuba a kwano, zuba yoghurt akai da flavour ,suger da kuma kankara,za ’ a sha da sanyi.
<¤ BREAK FAST NOG
Kayan hadi : -
•Madara
•leman zaki
•yoghurt
• nutmeg
• ayaba
• suger
YADDA AKE HADAWA
Zuba leman zaki,ayaba , madara da yoghurt a cikin blender idan sun markadu sosai juye a jug,za ’a sa a frig(Refrigerator ) ko a zuba kankara, zuba nutmeg akai idan kanaso .
¤ TAMARING JUICE
Kayan hadi : -
• Tsamiya
• Suger
•Kanunfari
•Citta
• leman tsami
YADDA AKE HADAWA
dafa suger da ruwa barshi ya huce . dafa tsamiya da ruwa , kanunfari da citta har misalin minti 30 .
tace tsamiyar abarshi ya huce yayi sanyi .
matse leman tsami a kuma yanka guda biyu yankan fadi .
hada dafaffan suger acikin tsamiya zuba leman tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.
asaka cikin frig (Refrigerator ) yayi sanyi sosai kafin sha.
zaka zuba ruwa dai dai tsamin da kakeso kafin sha.
¤ ICEE TEA
Kayan hadi : -
• Ganyan shayi
• Suger
• Leman tsami
• Na’a - na ’a
• Kanunfari
YADDA AKE HADAWA
Za ’a dafa duka kayan amma banda suger da leman tsami.
dafa suger da ruwa .
matse leman tsami a kofi ajiye gefe daya .
Tace ganyan shayi da rariya, zuba suger da leman tsami.
Saka cikin frig(Refrigerator ) yayi sanyi sosai .
Idan za ’a sha saka ganyan na ’a- na ’a da aka tsinka guda biyar a ciki da leman tsamin da aka yanka akekkewayo a ciki .
a kuma dauki slice daya a yanka bakinsa kadan a saka ajikin bakin kofin .
Za ’a sha da strew.
¤ PINACOLADO
Kayan hadi: -
•Kwakwa
•Abarba ko leman zaki
• Suger
•Flavour na abarba
YADDA AKE HADAWA
Za ’a goga kwakwa da abun goga kubewa ,markada a blender sai a zuba ruwan sanyi a tace da rariya.
markada abarba ko [leman zaki] taceta zuba a kwano.
dafa suger da ruwa barshi ya huce .
Hada kwakwa da abarba guri daya ko leman zaki zuba suger da flavour juya sosai asa a frig(Refrigerator ) yayi sanyi . wannan leman ana hadashi ne lokacin da za ’ a sha.
idan kuma aka hada aka sa shi a frig(Refrigerator ) za ’ a ga man kwakwar ya taso ,ba lalace wa yayi ba sai akara markadawa .
¤ FRUIT SALAD
Kayan hadi : -
•Abarba
• Gwanda
• Ayaba
•Kankana
•Leman zaki
• Kwakwa
•Leman tsami
• Suger
YADDA AKE HADAWA
za ’ a yanka duk kayan marmarin kanana - kanana(cubes ).
Za ’a bare leman zaki sala - sala sannan acire kwallon a zubar ,a tara totuwar leman da ruwan leman a kofi .
Goga kwakwa kanana .
Matse leman tsami a kwano, yanka ayaba kanana - kanana sai a zuba cikin leman tsami (yin haka yana hana ayabar tayi baki). Dafa suger da ruwa ajiye gefe daya.
Za’ a hada duka yankakkun kayan marmarin waje daya acikin abun da ake hada fruit salad .
zuba suger aciki juya sosai .
Idan za ’a sha zaka iya zuba condensed milk akan fruits din .
¤ FRUIT DRINK
Za ’ ayi amfani da duka kayan marmarin da muka yi amfani da su a sama. Za ’a zuba a cikin blender a markada su . Tace da rariya mai laushi (kara ruwa idan kina bukata). Zuba suger yadda kakeso ( Idan kina da bukata zuba masa madara).