6 Feb 2018

YANDA AKE WAINAR HANTA

WAINAR HANTA
ABIN BUKATA:-
Hanta
Magi
Gishiri
Kori
Albasa
Tumatur
Kwai
Man gyada
Kayan miya

HADI:-
Xamu tafasa hanta da gishiri da albasa idan ya dahu, sai mu daka ta da turmi , idan ta daku sai mu kwashe, sai mu kawo markadan mu kamar cokali biyu na miyan ki xuba kisa magi da gishiri da kori sai ki tafasa kwai ki yanka albasa da dan attarugu sai ki hada ki juya sosai to sai ki dora man ki a wuta ki fara xuba wannan kullin akan tiran kamar yadda akeso soya wainar fulawa idan kin gama sai ki kwashe.
misali : - Anta daya magi uku kwai uku kayan miya biyar kori 1 / 2 cokali munayi naku fatan alhkairi

© GIDAN AURE 

No comments:

Post a Comment