12 Sept 2018

Sarki Daya Ne Kacal A Kannywood Inji Adam Zango

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango ya bayyana cewa sarki kwaya daya tal ne kawai a masana’antar Kanyywood da ke shirya fina-finan Hausa.

Adam Zango ya bayyana hakan ne a shafukansa na kafofin sadarwa na zamani, inda ya nuna cewa har yanzu Ali Nuhu ne sarki.

Daga baya kuma sai ya saka wani hoto, inda yake zugunne a gaban Ali Nuhu, shi kuma Ali yana zaune a kan kujera, sai ya rubuta cewa ‘tuba nake sarki’.

Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wasu suke ganin akwai takun saka tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu, wanda har ake tunanin yadda za a samar da zaman lafiya na dindindin a tsakaninsu.

No comments:

Post a Comment