22 Sept 2018

[Audio] Baba Buhari Mai Kasa 2019 - Afandaj

Ga Wata Sabuwar Waka Mai Taken Baba Buhari Mai Kasa 2019  Wanda Mawaki  Mai Suna  Afandaj Yayi

Download Now

20 Sept 2018

[Audio] Malam Yayiwa Tsula Wayau - Dauda Rarara

Mawaki Rarara Ya Kara Sakin Wata Sabuwar  Waka Mai Taken Malam Yayiwa Tsula Wayau.


Download Now



Daga: Presshausa.com

18 Sept 2018

Babban Dalilin Da Yasa Na Daina Fitowa A Fim - Inji Zainab Indomie

Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta.

Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai.

Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu.

Sai dai tana tsakiyar tashe aka daina jin duriyar jarumar, abin da ya kai ga ana diga ayar tambaya da yada jita-jita a kan dalilan daina ganinta a fina-finai.

"A lokacin da jarumar ke kan ganiyarta kusan ana iya cewa ta yi wa sauran matan wannan masana'antar fintinkau", a cewar Kabiru Jammaje, wani mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood.

Jammaje ya ce akwai daraktoci da masu shirya fina-finan wadanda yanzu haka suka shirya su yi aiki da Indomie saboda hikima da kuma kwarewarta a harkar fina-finai.

Mece ce hakikanin abin da ya boye Indomie?
Daina fitowar Indomie a fina-finai ya ja hankalin masoyan fina-finan Hausa, har aka rika danganta hakan da wasu bayanai da halayen da ake ganin su suka tilasta mata daina fitowa a fina-finai.

Sai dai Zainab Indomie ba ita ce jarumar Kannywood ta farko da ta daina haskawa a fina-finan ba, akwai da dama irinsu Kubura Dhako da Ummi Nuhu da Saima Muhammad da Ummi Zee-zee da dai sauransu.

Ko da yake akwai tsoffin jarumai irinsu Safiya Musa da Fati Ladan da Zainab Raga da aure ne ya boye su.

A tattaunawarta da BBC Indomie ta karyata dukkanin rade-radin da ake yi a kanta, ta kuma shaida cewa kawai ta yanke shawarar tafiya hutu ne domin dagawa 'yan baya kafa.

"A kowanne lokaci ana son wani ya bai wa wani dama don shi ma ya samu lokacin damawa, don in da ina tsaye a kan karagata da ban bai wa 'yan baya dama ba.

"Na dawo bakin sana'a ta wadda In Allah Ya yarda idan aka ga na koma to sai dai idan aure ne", inji Indomie

Zainab Indomie ta ce a yanzu takamaimai ba za ta iya cewa ga fim din da za a soma ganinta a cikinsa ba, sai dai ana tuntubar ta kuma a cikin wannan watan ma akwai shirin fim da take aiki a kan shi.

Labarin dawowarta fina-finai ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman shafin Instagram bayan da fitattun jarumai irinsu Adam A. Zango da Ali Nuhu suka wallafa hotunanta don taya ta murnar dawowa masana'antar.

Kabiru Jammaje, wanda ke shirya fina-finan Turanci a Masana'antar Kannywood, ya ce yanzu haka akwai wani shirin fim na Ingilishi da yake shirin haska Jarumar.

Akwai soyayya tsakanin Indomie da Zango?
An sha yada jita-jitar soyayya a tsakanin Adam A. Zango da Zainab Indomie; ko a wannan lokacin wasu na ganin cewa shi ya taimaka mata sake dawowa bakin sana'arta.

Amma Indomie ta ce: "Ni na dauki Adamu ubangida na ne kuma kamar dan uwa na dauke shi kamar yadda ya dauke ni amma babu komai tsakani na da shi.

"Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana'a".
Indomien dai ta ce ba ta da wani buri da ya wuce samun miji na gari ta yi aure.

Daga Bbchausa

[Audio] Ku Fahimce Buhari Talakawa - Rarara

Sabuwar Wakar Dauda Kahutu Rarara Mai
Taken Ku Fahimce Buhari Talakawa
Ku Danna Download Domin Dauko Wa

Download Now

14 Sept 2018

[Waka] Ja Muje Baba Aminu Masari Gwamnan Katsina 2019

Sabuwar Waka Da Akayi Ma Aminu Bello Masari Gwamnan Jihar Katsina Mai Taken Ja Muje Baba Masari 2019.

Wakar Tana Da Dadi

Download Now

12 Sept 2018

Sarki Daya Ne Kacal A Kannywood Inji Adam Zango

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango ya bayyana cewa sarki kwaya daya tal ne kawai a masana’antar Kanyywood da ke shirya fina-finan Hausa.

Adam Zango ya bayyana hakan ne a shafukansa na kafofin sadarwa na zamani, inda ya nuna cewa har yanzu Ali Nuhu ne sarki.

Daga baya kuma sai ya saka wani hoto, inda yake zugunne a gaban Ali Nuhu, shi kuma Ali yana zaune a kan kujera, sai ya rubuta cewa ‘tuba nake sarki’.

Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wasu suke ganin akwai takun saka tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu, wanda har ake tunanin yadda za a samar da zaman lafiya na dindindin a tsakaninsu.

5 Sept 2018

An Kama Ma'aikacin Bogi Na EFCC A Majalisar Dokokin Jihar Adamawa

An kama wani ma'aikacin EFCC na karya a jihar Adamawa a gidan gwamnati jihar Adamawa, inda yaje yana Kokarin kama wani Dan Majalisar Dokokin Nijeriya..

2 Sept 2018

Dalilin Da Yasa Nake Yiwa Mata Waka - Ado Gwanja

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

Gwanja: An haife ni a Unguwar Birged da ke birnin Kano. Sai dai asalin mahaifina dan garin Warawa ne, yayin da mahaifiyata Shuwa Arab ce daga garin Maiduguri a Jihar Borno.

Na yi karatun firamare a Makarantar Babbangiji da ke Karkasara. Sannan na yi sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa. Bayan na gama ban ci gaba da karatu ba sai na rika zuwa kasuwa wurin mahaifina.

Bayan mahifina ya rasu ne sai na shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo ni matsayin da nake a yanzu.

Mutane da dama sun san Gwanja a fina-finan Hausa sai kuma ga shi ka canja sheka zuwa waka, yaya aka yi hakan ta kasance?

Gwanja: To a gaskiya dama waka na fara, domin na fi shekara 12 ina yin waka, sai dai a wancan lokaci ba a san ni ba. A wancan lokaci nakan rubuta waka tun ba ni da kudin zuwa situdiyo na buga har na rika zuwa ina bugawa. Ko ta yi dadi ko ba ta yi ba ban damu ba, ni dai na san ina waka. To bayan wani lokaci kuma sai na shiga harkar fim.

Yawancin lokuta an fi ganin kana fitowa a matsayin dan Daudu a fina-finan Hausa, haka ka fi mika akalar wakokinka a kan mata, me ya jawo haka?

Gwanja: To batun fina-finai da nake yi a dan Daudu wannan yanayin labari ne ya zo da haka, kasancewar na yi abin da ake bukata a wasu fina-finai da aka ba ni wannan matsayi to sai ya zama cewar in dai labari ya zo da hakan sai a nemo ni a ba ni. Amma ba ni nake zabe ba.

Shi kuma batun waka da ake ganin na fi yi wa mata, zan iya cewa saboda su ne iyayen biki.

Bahushe ya ce inda baki ya karkata ta nan yawu kan zuba. Kowa ya san irin rawar da mata ke takawa idan aka zo harkar biki, kin ga kuwa tunda ina yin wakokin biki, to dole da su za a yi.

Baya ga wakokin fina-finai da kake yi da na biki kana yin wakikin siyasa?

Gwanja: Eh ina yin wakoki ga ’yan siaysa, idan dan siyasar da kansa ya nemi hakan. Abin da ba na yi shi ne ba na yin waka in kai wa dan siyasa, saboda na san halinsu sai a hankali.

Yaya dangantakarka da sauran mawaka?

Gwanja: Gaskiya akwai alaka mai kyau a tsakaninmu, don akwai girmamamawa a tsakninmu.

Ba ma yi wa juna hassada ko bakin ciki.

Wane ne gwaninka a fagen wakoki?

Gwanja: Ba ni da gwanin da ya wuce Aminu Maidawayya.

Kasancewar an fi daukarka don yin wasa a bukukuwan aure, mutane na zargin cewa ba ka zuwa biki ko amsa gayyatar talakawa, mece ce gaskiyar wannan batu?

Gwanja: Gaskiya abin ba haka yake ba. Ai abin ba kudi ba ne, domin wani ma za ka iya yi masa kyauta ya danganta da yanayin mu’amalarku.

Ina ganin duk mutumin da ya zo ku yi mu’amala ya mutunta ka, domin a da bai zo wurinka ba. Haka kuma wata rana ba zai zo wurin naka ba. Kawai ni abin da na sani shi ne ba a fin karfin masoyi.

Masu yin wadannan kalaman suna yi ne don ba a yi musu kyauta-kyauta ba ko kuma ma kai-tsaye in ce kyauta. Kowace sana’a sunanta sana’a dole mutum ya yi hakuri ya bi yaddda tsarin abu yake wajen.

Wane tallafi mawaka ke samu daga gwamnati?

Gwanja: Ni zan iya cewa tsawon rayuwarta a wannan fage ban taba jin labarin gwamnati ta ba mu tallafi ko wani abu makamancin haka ba. Idan ka ga gwamnati ta waiwaye mu, to so take ta yi amfani da mu don cimma wata bukatarta ko kuma idan ana neaman mu biya haraji.

Gwamnati ba ta kallonmu a matsayin wadanda suka rage mata nauyin neman aiki, domin akalla ban da nauyin kanmu da muke dauka muna da yara da ke aiki a karkashinmu wadanda ta nan suke samun abin da suke kula da iyalansu.

Daga: Jaridar Aminiya