22 Aug 2018

Zamu Yaki APC Sabida Rashin Cika Alkawarinta -Inji Yan Fim

Wadansu daga cikin ’yan fim din Hausa a karkashin jagorancin Furodusa kuma Darakta, Usman Mu’azu sun kafa wata kungiya mai taken Kannywood PDP Support Forum (KPSF), inda za su rika yi wa ’yan takara a PDP kamfe.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Usman Mu’azu ya bayyana dalilinsu na kafa kungiyar da dalilin da ya sa za su yi wa Jam’iyyar PDP kamfe duk da ana yi mata kallon jam’iyyar ’yan cin hanci da rashawa. Kuma ya bayyana abubuwan da ’yan fim suke so Jam’iyyar PDP ta yi musu idan ta yi nasara a zaben 2019. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me ya ja hankalinku kuka kafa kungiyar taku?

A gaskiya da ma can mu ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne, kuma mun dade muna yi wa PDP gwagwarmaya, mun dade muna yi mata aiki, kuma sai muka ga tunda zaben 2019 ya gabato, to ya kamata mu kara yin kira don mu hada kanmu, domin mu bai wa jam’iyyar da muke cikinta gudunmawa, saboda muna sa ran insha Allahu a 2019, ita ce mafita ga ’yan Najeriya.

Zuwa yanzu kuna da mambobi nawa?

Akalla yanzu akwai mutum sama da 37 da suke karkashin wannan tafiya, kuma duka ’yan Kannywood ne da suka hada da furodusoshi da daraktoci da mawaka da jarumai, kadan daga cikinsu akwai Halima Atete da Fati Muhammad da Asma’u Sani da furodusa ABS Bafarawa, wanda shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar, sannan akwai mawaki Abubakar Sani da sauransu.

A yanzu mun fara ziyartar jiga-jigan jam’iyyarmu, kasancewar mun ce da ma za mu rika zama da masu fada a cikin jam’iyyarmu ta PDP, za mu je mu gabatar musa da kanmu, mu kuma gabatar masa da kudurinmu, sannan kamar yadda muke sa ran za a samar da mafita, to mu kofa a bude take a duk lokacin da bukatar aikinmu ya zo, za mu shiga mu ba da gudunmawarmu, da ta hada da lokacinmu da karfinmu da iliminmu da kudinmu a cikin wannan tafiya domin wannan tafiyar tamu ta kai ga gaci.

A kwanakin baya kun kai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ziyara, me kuka tattauna a lokacin?

Mun ji dadi sosai da wannan ziyarar, kusan da ma shi Malam Ibrahim Shekarau shi yake bin mu bashi, ba mu ke bin sa bashi ba.

Idan na ce shi yake bin mu bashi a karkashin wannan tafiya tamu a PDP da kuma ta masana’antar fim ta Kannywood, kusan zan ce Malam Ibrahim Shekarau ya yi mana abin da zan ce har gobe yake bibiyarmu a masana’antar fim. Ya ba da gudunmawa wajen tsabtace ita kanta harkar fim.

Shi ne mutum na farko da ya fara taimakon masana’antar da abin hawa a lokacin da muka nema. Shi ne mutum na farko da ya fara karrama ’yan fim a cikin gwamnonin Kano.

Shi ne mutum na farko da ya fara shirya taron kara wa juna sani don wayar da kan mutane kan ita kanta yadda sana’ar fim take.

A zaman da muka yi da Shekarau, ya nanata godiyarsa gare mu, kuma ya daukar mana alkawarin cewa duk lokacin da bukatarsa ta taso a tafiyarmu, to kofa a bude take, shi mahaifinmu ne.

Shekarau ya ce kuma duk wani dan Jam’iyyar PDP to ya matso kusa da ’yan fim domin in ka nesanta kanka da mu, ba za ka san matsalolinmu ba, ba za ka san abin da muke iya koyarwa na alheri ba, ba za ka san abin da muke yi na kuskure ba. Idan da iyayenmu a ciki irin su Shekarau din, to za a samu raguwar duk wasu abubuwa da ake yi na kuskure, domin idan suka ga an yi kuskure to za su kira mu su ba mu shawara, za su kuma saita mu a hanyar da ta dace.

Bayan Shekarau, ko akwai wadansu jiga-jigan PDP da kuke shirin kai musu irin wannan ziyara?

Bayan Malam Ibrahim Shekarau mun fitar da sunayen jiga-jigan PDP da za mu kai wa ziyara, domin shi kansa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Mukhtar Ramalan Yero ma mun zauna da shi, kuma ya fada mana cewa kofa a bude take don ya taimaka mana a duk lokacin da bukatar taimakon ta taso, shi ma yana daya daga cikin wadanda suka ba mu gudunmawa a baya.

Domin duk wani taro da za mu yi wanda zai ciyar da masana’antarmu gaba, to a baya yana sa kansa a ciki, kuma ya nanata zai ci gaba da yin haka.

Sannan daga cikin wadanda za mu gana da su akwai Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus da Shugabar Mata ta kasa ta PDP da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa da Kabiru Tanimu Turaki, wanda yake neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP da Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan dankwambo da tsohon Gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema da tsohon Ministan Abuja, Bala Muhammad da sauransu.

A Arewa dai tuni mun fitar da sunayen wadanda za mu gana da su, tuni mun tura musu da takardu.

Wadanne abubuwa ne kuke so a yi muku idan jam’iyyarku ta PDP ta kai ga nasara a zaben 2019?

Akwai abubuwa da dama da muke ganin su ne matsalolinmu, akwai abin da ya faru a wannan gwamnati mai ci yanzu, na kokarin da ta yi wajen gina mana alkaryar daukar fim, abu ne wanda muke sa ran idan an killace mu to harkar fim za ta sake samun tsabta, kuma sai ya kasance gwamnati ba ta ba da gudunmawa ba wajen ganin cewa abin da aka kawo an tabbatar da yiwuwarsa.

Sai muke ganin idan jam’iyyarmu ta dawo kan mulki, muke so ta gina mana alkaryar daukar fim, domin wata hanya ce da za a kara tsabtace harkar da kara inganta harkar da kayan aikin da kasashe da dama suke amfani da su, inda har yanzu wadannan kayayyaki ba su zo gare mu ba.

Muna so gwamnatin PDP idan ta dawo kan mulki, to ta debi wadansu daga cikin mutanenmu ta kai su don su karo ilimi, kasancewar kullum duniya ana kara ci gaba ne.

A matsayina na dan PDP ba zan ce wannan jam’iyya ba ta yi mana komai ba, akwai abubuwan da ta taimaka, to ta yi daidai nata, muna so idan ta dawo to za ta taimaka fiye da wannan gwamnati da take kai a yanzu.

Muna so gwamnati ta samar da kayan aiki da jari da kuma bashi marar ruwa ga ’yan fim, ba wai mu ’yan kungiya ba kawai, kowane dan fim, bukatarmu ita ce da wanda yake dan PDP da wanda yake ba dan PDP ba in dai a Kannywood yake, to ya samu ci gaba.

Jama’a da dama suna alakanta mambobin jam’iyyarku ta PDP da cin hancin da rashawa, kuma ga shi za ku yi wa PDP kamfe, kuna ganin za ku kai ga nasara?

Shi dan Adam mai kuskure ne, kuma ba za mu ce haka ba, abin da yake kara kulle mana kai shi ne, wai shin Jam’iyyar PDP ce kadai a Najeriya wadda ake zarginta da cin hanci da rashawa? To a gaskiya ba mu gamsu da hakan ba, kuma ba a yi mana adalci ba, tunda a kowace sana’a, a kowace tafiya, sannan a kowace jam’iyya akwai masu aikata kura-kurai. Akwai jam’iyyu da dama da ake gani a fili a yanzu ba zan kai ga fadin sunayensu ba saboda wadansu dalilai, amma idan hali ya yi, za mu kai ga fadar jam’iyyun da kuma mutanen da muke zarginsu da cin hanci da rashawa.

Kuma ina so mutane su fahimta har yanzu kotu ba ta kai ga kama su da laifi ba, wadanda ma aka yanke wa shari’a ’yan Jam’iyyar APC ne, wato tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame da kuma tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye.

Na jam’iyyarmu zarginsu ake yi, kuma har yanzu suna zuwa kotu, wadansu daga cikin ’yan jam’iyyarmu ma shari’arsu ta mutu, saboda abin da ake zarginsu da shi ba gaskiya ba ne.

Don haka za mu yi wa PDP kamfe, kuma idan muka kai ga nasara za a fahimci jam’iyyarmu da aka shafa mata kashin kaji na cin hanci da rashawa ba fa haka take ba, wadansu kuma za su fahimci da ma dole a cikin nagari sai an samu batagari.

Daga: Jaridar Aminiya

No comments:

Post a Comment