29 Aug 2018

[Waka] Non-Stop - Rhombooz

The Katsina finest Ibrahim Rhombooz aka Arewa No.1 is back with the first single of his sophomore mixtape "StreetEmpire" which will be released early next year.

This track Non Stop has featured the newly signed artist of BLD "Lil Ussy" and Rhombooz sounds to be Non stop according to the lines he dropped in this collabo

Kindly download listen and share it's a hit.

Twitter/Instagram: @Iam_Rhombooz
Facebook: @ Ibrahim Rhombooz

Download Now

28 Aug 2018

An Hana Kwankwaso Taron Kaddamar Da Neman Takarar Shugaban Kasa A Abuja

Kasa da awa 24 kafin lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya fito domin kaddamar da kan sa neman takarar shugabancin kasa, karkashin jam’iyyar PDP, hukumomi sun hana shi yin amfani da Dandalin ‘Eagle Square’, wanda tun da farko a can ne aka shirya za a gudanar da gangamin.

Haka kuma majiyarmu ta samu labarin cewa an hana Kwankwaso yin amfani da Tsohon Filin Faretin Abuja, da ke daura da Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa.

Kwankwaso wanda kwanan nan ya fice daga APC ya koma PDP, ya sanar da cewa a gobe Laraba ne zai kaddamar da neman fitowa takarar shugabancin kasar nan a fafata da shi a karkashin jam’iyyar PDP.

Cikin wata wasika da manajan filin taro na ‘Eagle Square da International Conference Centre,’ mai suna Usman Raji ya sa wa hannu, ta ce an hana Kwankwaso gudanar da taron ne a Eagle Square, domin kada cinkoson jama’a ya hana ma’aikatan gwamnati zirga-zirga da gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata.

Ya ce a nan ne Sakateriyar Gwamnatin Tarayya ta ke, inda nan ne dandazon rukunin ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma dubban ma’aikatan gwamnati suke.

Usman Raji ya ba su hakuri tare da cewa hakan ya faru ne saboda an aza ranar taron ne ta yi daidai da ranar aiki.

Sai dai Tawagar Kamfen din Kwankwaso ta ce wannan wata manakisa ce daga gwamnati saboda ba ta son duk wani ci gaba na dimokradiyya.

Sun shaida cewa tun kafin su shirya wannan taro a filin ‘Eagle Square’ sai da suka biya kudin da ke biya domin hayar wannan fili, sannan kuma ko a wancan lokaci ba a ce musu baza a basu ba.

” Kwatsam sai gashi yanzu an ce wai saboda tsaro da walwalan ma’aikatan gwamnati an hana mu wannan fili.”

Da muka nemi ji daga bakin ministan Abuja, kakakin sa ya ce minista Abubakar Bello ba shi da masaniya a kai.

Ita ma Binta Sipikin, wato kakakin Kwankwaso bata ce komai a kai ba tukunna.

23 Aug 2018

Rikicin Tsakinin Tsohuwar Jaruma Rukayya Dawayya Da Wata Jarumar Fim

Daya daga cikin fitattun tsaffin fuskokin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood mai suna Rukayya Umar Santa da aka fi sani da Rukayya Dawayya ta nuna rashin jin dadin ta game da wata sabuwar jarumar fim din da ta nuna bata san ta ba.

Mun samu cewa duk da yake dai bata kama suna ba, amma dai da alama sabuwar jarumar ta bata mata rai sosai inda har hakan ya ja ta tunzura ta ta kuma huce haushin ta a dandalin sada zumuntar.

Ga dai abun da ta fada nan:

"Bude idonki sosai ki ganni. karyane kice kina masana antar kannywood baki sanni bah. kokice bakisan sunana bah wlh karya kike. daga 10 years zuwa yanzu duk wacce ta shigo industry mutagani tashigo. idan kinzo da Alkhairi kiga Alkhairi idan kinshigo da sharri ko kwadayi duk kigani a kwaryar shanki. karyar banza. sorry my fan's wata banzace tabani haushi."

22 Aug 2018

Zamu Yaki APC Sabida Rashin Cika Alkawarinta -Inji Yan Fim

Wadansu daga cikin ’yan fim din Hausa a karkashin jagorancin Furodusa kuma Darakta, Usman Mu’azu sun kafa wata kungiya mai taken Kannywood PDP Support Forum (KPSF), inda za su rika yi wa ’yan takara a PDP kamfe.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Usman Mu’azu ya bayyana dalilinsu na kafa kungiyar da dalilin da ya sa za su yi wa Jam’iyyar PDP kamfe duk da ana yi mata kallon jam’iyyar ’yan cin hanci da rashawa. Kuma ya bayyana abubuwan da ’yan fim suke so Jam’iyyar PDP ta yi musu idan ta yi nasara a zaben 2019. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me ya ja hankalinku kuka kafa kungiyar taku?

A gaskiya da ma can mu ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne, kuma mun dade muna yi wa PDP gwagwarmaya, mun dade muna yi mata aiki, kuma sai muka ga tunda zaben 2019 ya gabato, to ya kamata mu kara yin kira don mu hada kanmu, domin mu bai wa jam’iyyar da muke cikinta gudunmawa, saboda muna sa ran insha Allahu a 2019, ita ce mafita ga ’yan Najeriya.

Zuwa yanzu kuna da mambobi nawa?

Akalla yanzu akwai mutum sama da 37 da suke karkashin wannan tafiya, kuma duka ’yan Kannywood ne da suka hada da furodusoshi da daraktoci da mawaka da jarumai, kadan daga cikinsu akwai Halima Atete da Fati Muhammad da Asma’u Sani da furodusa ABS Bafarawa, wanda shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar, sannan akwai mawaki Abubakar Sani da sauransu.

A yanzu mun fara ziyartar jiga-jigan jam’iyyarmu, kasancewar mun ce da ma za mu rika zama da masu fada a cikin jam’iyyarmu ta PDP, za mu je mu gabatar musa da kanmu, mu kuma gabatar masa da kudurinmu, sannan kamar yadda muke sa ran za a samar da mafita, to mu kofa a bude take a duk lokacin da bukatar aikinmu ya zo, za mu shiga mu ba da gudunmawarmu, da ta hada da lokacinmu da karfinmu da iliminmu da kudinmu a cikin wannan tafiya domin wannan tafiyar tamu ta kai ga gaci.

A kwanakin baya kun kai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ziyara, me kuka tattauna a lokacin?

Mun ji dadi sosai da wannan ziyarar, kusan da ma shi Malam Ibrahim Shekarau shi yake bin mu bashi, ba mu ke bin sa bashi ba.

Idan na ce shi yake bin mu bashi a karkashin wannan tafiya tamu a PDP da kuma ta masana’antar fim ta Kannywood, kusan zan ce Malam Ibrahim Shekarau ya yi mana abin da zan ce har gobe yake bibiyarmu a masana’antar fim. Ya ba da gudunmawa wajen tsabtace ita kanta harkar fim.

Shi ne mutum na farko da ya fara taimakon masana’antar da abin hawa a lokacin da muka nema. Shi ne mutum na farko da ya fara karrama ’yan fim a cikin gwamnonin Kano.

Shi ne mutum na farko da ya fara shirya taron kara wa juna sani don wayar da kan mutane kan ita kanta yadda sana’ar fim take.

A zaman da muka yi da Shekarau, ya nanata godiyarsa gare mu, kuma ya daukar mana alkawarin cewa duk lokacin da bukatarsa ta taso a tafiyarmu, to kofa a bude take, shi mahaifinmu ne.

Shekarau ya ce kuma duk wani dan Jam’iyyar PDP to ya matso kusa da ’yan fim domin in ka nesanta kanka da mu, ba za ka san matsalolinmu ba, ba za ka san abin da muke iya koyarwa na alheri ba, ba za ka san abin da muke yi na kuskure ba. Idan da iyayenmu a ciki irin su Shekarau din, to za a samu raguwar duk wasu abubuwa da ake yi na kuskure, domin idan suka ga an yi kuskure to za su kira mu su ba mu shawara, za su kuma saita mu a hanyar da ta dace.

Bayan Shekarau, ko akwai wadansu jiga-jigan PDP da kuke shirin kai musu irin wannan ziyara?

Bayan Malam Ibrahim Shekarau mun fitar da sunayen jiga-jigan PDP da za mu kai wa ziyara, domin shi kansa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Mukhtar Ramalan Yero ma mun zauna da shi, kuma ya fada mana cewa kofa a bude take don ya taimaka mana a duk lokacin da bukatar taimakon ta taso, shi ma yana daya daga cikin wadanda suka ba mu gudunmawa a baya.

Domin duk wani taro da za mu yi wanda zai ciyar da masana’antarmu gaba, to a baya yana sa kansa a ciki, kuma ya nanata zai ci gaba da yin haka.

Sannan daga cikin wadanda za mu gana da su akwai Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus da Shugabar Mata ta kasa ta PDP da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa da Kabiru Tanimu Turaki, wanda yake neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP da Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan dankwambo da tsohon Gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema da tsohon Ministan Abuja, Bala Muhammad da sauransu.

A Arewa dai tuni mun fitar da sunayen wadanda za mu gana da su, tuni mun tura musu da takardu.

Wadanne abubuwa ne kuke so a yi muku idan jam’iyyarku ta PDP ta kai ga nasara a zaben 2019?

Akwai abubuwa da dama da muke ganin su ne matsalolinmu, akwai abin da ya faru a wannan gwamnati mai ci yanzu, na kokarin da ta yi wajen gina mana alkaryar daukar fim, abu ne wanda muke sa ran idan an killace mu to harkar fim za ta sake samun tsabta, kuma sai ya kasance gwamnati ba ta ba da gudunmawa ba wajen ganin cewa abin da aka kawo an tabbatar da yiwuwarsa.

Sai muke ganin idan jam’iyyarmu ta dawo kan mulki, muke so ta gina mana alkaryar daukar fim, domin wata hanya ce da za a kara tsabtace harkar da kara inganta harkar da kayan aikin da kasashe da dama suke amfani da su, inda har yanzu wadannan kayayyaki ba su zo gare mu ba.

Muna so gwamnatin PDP idan ta dawo kan mulki, to ta debi wadansu daga cikin mutanenmu ta kai su don su karo ilimi, kasancewar kullum duniya ana kara ci gaba ne.

A matsayina na dan PDP ba zan ce wannan jam’iyya ba ta yi mana komai ba, akwai abubuwan da ta taimaka, to ta yi daidai nata, muna so idan ta dawo to za ta taimaka fiye da wannan gwamnati da take kai a yanzu.

Muna so gwamnati ta samar da kayan aiki da jari da kuma bashi marar ruwa ga ’yan fim, ba wai mu ’yan kungiya ba kawai, kowane dan fim, bukatarmu ita ce da wanda yake dan PDP da wanda yake ba dan PDP ba in dai a Kannywood yake, to ya samu ci gaba.

Jama’a da dama suna alakanta mambobin jam’iyyarku ta PDP da cin hancin da rashawa, kuma ga shi za ku yi wa PDP kamfe, kuna ganin za ku kai ga nasara?

Shi dan Adam mai kuskure ne, kuma ba za mu ce haka ba, abin da yake kara kulle mana kai shi ne, wai shin Jam’iyyar PDP ce kadai a Najeriya wadda ake zarginta da cin hanci da rashawa? To a gaskiya ba mu gamsu da hakan ba, kuma ba a yi mana adalci ba, tunda a kowace sana’a, a kowace tafiya, sannan a kowace jam’iyya akwai masu aikata kura-kurai. Akwai jam’iyyu da dama da ake gani a fili a yanzu ba zan kai ga fadin sunayensu ba saboda wadansu dalilai, amma idan hali ya yi, za mu kai ga fadar jam’iyyun da kuma mutanen da muke zarginsu da cin hanci da rashawa.

Kuma ina so mutane su fahimta har yanzu kotu ba ta kai ga kama su da laifi ba, wadanda ma aka yanke wa shari’a ’yan Jam’iyyar APC ne, wato tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame da kuma tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye.

Na jam’iyyarmu zarginsu ake yi, kuma har yanzu suna zuwa kotu, wadansu daga cikin ’yan jam’iyyarmu ma shari’arsu ta mutu, saboda abin da ake zarginsu da shi ba gaskiya ba ne.

Don haka za mu yi wa PDP kamfe, kuma idan muka kai ga nasara za a fahimci jam’iyyarmu da aka shafa mata kashin kaji na cin hanci da rashawa ba fa haka take ba, wadansu kuma za su fahimci da ma dole a cikin nagari sai an samu batagari.

Daga: Jaridar Aminiya

21 Aug 2018

Abinda Gwamnatin Shugaban Buhari Yakamata Yayiwa Yan Fim - Al'amin Buhari

Al-Ameen Buhari yana daya daga cikin manyan jaruman masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, a hirar da Aminiya ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ya fara harkar fim da kalubalen da yake fuskanta a masana’antar da yadda ya sa aka sauke masa Alkur’ani kafin ya shiga harkar fim, inda ya ce fim ya yi masa riga da wando:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Al-Ameen Buhari, an haife ni a garin Jos, na yi karatun boko da na addini daidai gwargwardo. Na yi karatun kur’ani da hadisai a Lafiya da ke Jihar Nasarawa. A bangaren karatun boko kuwa na tsaya a sakandare ne, kafin in shiga harkar fim ina sana’ar tukin babbar mota ce, daga baya na fara harkar fim. Ina da mace daya da ’ya’ya biyar, inda na aurar da ’yata ta farko kuma a yanzu nake da jika.

Me ya ja hankalinka ka fara harkar fim?

Babban abin da ya ja hankalina na fara harkar fim shi ne, kamar yadda na gaya maka daga cikin tarihina, wato na yi karatun Muhammadiyya sosai, don har nakan fadakar da al’umma, ma’ana nakan yi wa’azi. A lokacin da harkar fina-finan Hausa ta fito sai na ga cewa wata hanya ce mafi sauki da mutum zai iya wa’azantarwa.

Idan ka kalli shirin fina-finanmu za ka ga daidai suke da wa’azantarwa, za ka ga mutum ya dauko rayuwa wacce ba hanyar Allah ba, daga karshe ya ga sakamako tun a duniya, daidai yake da malami ya ce ka bi Allah da Manzonsa (SAW), ka kyautata za ka ga sakamako mai kyau.

Ka zauna da makwabtanka da iyayenka za ka sakamakon hakan tun a duniya, haka a fim za ka mutum ya fito yana shaye-shaye ko bin mata ko kashe-kashe, za ka ga ko dai ya tuba, ko kuma karshensa ba zai zo da kyau ba, hakan sai ya sa na ce in na shiga harka fim to zan ba da gudunmawata wajen aika sakon zama lafiya da bin Allah da kyautata wa makwabta da sauransu.

Wane kalubale ka fuskanta lokacin da ka yi yunkurin shiga harkar fim?

A gaskiya ban fuskanci wani kalubale da zan ce ya takura wa rayuwata ba, dalili kuwa shi ne a shekarun baya kafin in shiga harkar zan iya tunawa wata rana ana nuna wani fim mai suna ‘Nazari’ a gidan silima na Kwararafa a nan Jos, a fim din akwai Ali Nuhu da Kumurci da Fati Muhammad da Abida Muhammad da sauransu, wanda ya shirya fim din shi ne Yusuf Khalid.

Shi kuma abokina ne, to fim din ya ba ni sha’awa, domin muna ta kallon fina-fina Indiya, muna kallon na Turai, a ranar kuma na kalli na Hausa kuma ya yi mini dadi, sai na je shagonsa bayan na kammala kallon fim din na ce masa duk lokacin da zai sake yin wani fim to ya sanya ni a ciki, domin ina da sha’awa. Sai ya ce idan zai sake wani to zai sa ni a ciki.

Haka na rika matsa masa, sai ya zamana na hadu da wani bawan Allah da yake neman mota za ta yi jigilar ’yan fim zuwa wurin daukar wani fim. Sai na ce masa ai dama ina da ra’ayin fim muka je wurin inda a nan na hadu da Salisu Mu’azu kanen Sani Mu’azu, bayan na yi masa magana sai ya ce mini zai shirya wani fim mai suna ‘Fargaba’. Da aka zo shirya fim sai aka fara gwada ni, sai ya ga abin nawa ya yi kyau, sai ya yi mini fatan alheri.

Kudin da ya biya ni a wancan lokacin sai na ce tun da wannan kudi ina da hanyar cin abincina, wannan wata sabuwar hanya ce, to bari na sa a roka mini Allah, in ba da sadaka da wannan kudi nawa na farko domin Allah Ya zama gata a tafiyar.

Aka sauke mini Al’kur’ani na yi sadaka da niyyar wannan sana’a da na sa ta niyyar fara fina-finai, to Allah Ya sa ta daure mini gindi, don in kai wani matsayi. Kuma alhamdulillahi na yi fina-finai masu muhimmanci, ina kuma jin dadinsu da kuma alfahari da su, saboda sakonnin da suka isar.

Ko ka san adadin fina-finan da ka yi kawo yanzu?

Magana ta gaskiya idan na hada kaina da manyan jarumanmu zan iya cewa ban yi wasu fina-finai masu yawa ba. Dalili da ban yi da yawa ba, saboda a nawa tsarin ba na karbar fim din da ba ya da ma’ana. Sa’annan kuma ba na yarda in yi aiki da daraktocin da ba za su tsaya su yi aiki mai kyau ba. Daraktocin da ba su yarda da aikinsu ba, za ka ga ba sa ma nemana.

A cikin fina-finan da ka yi zuwa yanzu wanne ka fi so, kuma me ya sa?

Zan iya fitar da fina-finai kamar uku, har kwanan gobe ina alfahari da su. Da farko akwai wani fim mai suna ‘Fari Da Baki’ na kamfanin darakta Aminu Saira, na ji dadin fim din saboda yadda sakon ya isa ga al’umma. Fim ne kan zamantakewar aure, na kasance ina da mace da mahaifiyata ba ta kaunarta, da ta zo sai ta ga matata da ciki, sai ta ce cikin ba nawa ba ne, domin zaman bai kai a samu ciki ba.

A fim din sai na biye wa mahaifiyata na ce cikin ba nawa ba ne, na sake ta, ta haifi dan, ni kuma na sake wani aure, matata kuma ta zo mini da dan da ba nawa ba, kuma na rungume shi. dana har ya girma na yi rashin lafiya aka kai ni asibitin da yake aiki, wato bayan ya zama likita ke nan, shi kuma wancan dan da ba nawa ba ina matukar sonsa, amma yana gana mini azaba.

Sai fim din ‘Ahlil Kitabi’ na Adam A Zango, fim ne na tarihi, inda yake da shigen kissar Annabi Yusuf (AS), na fito a cikin gefen ’yan uwan Annabi Yusuf, inda ni kuma na hau rol din kamar Yahuza, na rika gana wa Zango azaba, ina so fim din saboda sakon da ya isar.

Sai fim na uku wato ‘Azal’ na kamfanin 3SP wanda muka yi shi a nan Jos, na fito a matsayin azzalumin dan sanda, ga gaskiya amma saboda an ba ni cin hanci, sai in shafa wa idona toka, na rika gana wa mai gaskiya azaba, in yanka masa kazar wahala.

Yanzu za a iya cewa burinka ya cika a Kannywood?

Burina yana kan cika, zan iya cewa a cikin buri 10, to na samu bakwai, ina harin na takwas. A halin da ake ciki a yanzu ina da mata da ’ya’ya, cina da shana da suturata haka nasu, kula da lafiya da makarantarsu duk muna samu ne daga wurin Allah ta karkashin Kannywood. Na hau mota don alfarmar fim, na kwana a wuri mai kyau don alfarmar fim, fim ya yi mini riga da wando, shi nake yi yau da gobe. Abin da ya rage mini shi ne in mallaki gida nawa, in je aikin Hajji, sannan kuma in kara aure.

Zuwa yanzu wane kalubale kake fuskanta a Kannywood?

kalubalen da nake fuskanta a Kannywood ba ni kadai ba ne, mafi yawan ’yan fim suna fuskanta wannan kalubale, wato matsalar lalacewar kasuwa, ta taba kowa a Kannywood, wadda muna rokon Allah Ya kawo mana tallafi. Kuma muna rokon gwamnati ta kawo mana tallafi. Babu wanda ya san adadin wadanda suke ci a Kannywood, dubban mutane suke cin abinci a Kannywood, to ka ga an taimaki gwamnati wajen rage marasa aikin yi. Misali idan furodusa zai shirya fim na kwana bakwai, to za ka samu sama da mutum 150 suna cin abinci a karkashinsa, don haka ya kamata gwamnati ta taimaka wa ’yan fim.

Ya kamata gwamnatin Buhari ta taimaki ’yan fim saboda sun ba ta gudunmawa sosai, ta gyara mana masana’antarmu, ta ba mu jari, sannan ta yi mana yaki da masu satar fasaha.

Daga karshe wane sako kake da shi?

Wannan ya shafi abubuwan da suke faruwa a jihata, wato Filato da kuma karamar hukumata ta Jos ta Arewa, abubuwan da suke faruwa suna damuna, kuma babban abin yake kawo rashin ci gaba shi ne rashin zaman lafiya. Tun daga lokacin da aka kafa dimokuradiyya a 1999 zuwa yanzu mun yi gwamnoni uku, Dariye da Jang, yanzu kuma Lalong, ba mu taba samun Gwamnan da yake kokarin tabbatar da zaman lafiya kamar Lalong ba.

Ni ba dan siyasa ba ne, don haka idan Lalong bai yi kokari ba, to ba zan yabe shi ba, don haka ya kamata Musulmi da Kiristan Jihar Filato mu hada kai, sannan mu taimaka wa Lalong don a samu zaman lafiya.

Zaman lafiya zai kawo mana ci gaba sosai, kakan iya fita ka yi harkokinka ka dawo ba tare da dar-dar ba. Amma idan babu zaman lafiya hakan ba zai yiwu ba. Don haka idan aka yi tashin hankali babu abin da yake biyowa baya face talauci, don haka mu zauna lafiya da junanmu.

Daga : Jaridar Aminiya

19 Aug 2018

Na Rasa Meyasa Rayuwar Shirin Fim Dina Ta Lalace - Zainab Indomie

Fitacciyar jarumar da aka daina yayinta, Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yaya aka yi rayuwar aktin dinta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a masana’antar fina-finan Hausa.

Jarumar ta ce ta samu daukaka tun tana karama, amma saboda kaddara ba ta san abin da ya faru ba yanzu ta rasa komai.

Ta ce, “Na samu daukaka tuna ina karama, wani abu ya faru yanzu dai na rasa komai, babu ganganci a ciki, ba na kuma ganin laifin kowa, ban kuma zargi kowa ba sakamakon mawuyacin halin da na shiga.

“A halin da ake ciki ba zan iya tunawa da komai ba, ba zan iya cewa ga abin da ya sa na samu kaina a cikin mawuyacin hali ba. Idan har laifina ne ina rokon Allah Ya yafe mini, idan ma laifin wani ne to Allah Ya yafe masa,” inji ta.

Jarumar ta kuma roki Allah Ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya.
Ta ce, “Na gode wa Allah saboda jarrabawar da ya yi mini, ina rokon Allah Ya fitar da ni daga wannan jarrabawar. Na mika kaina ga hannun Ubangiji

Daga: Aminiya

18 Aug 2018

Mawaki Rarara Shine Yayi Mun Hanyar Shiga Shirin Fim Din Kannywood - Hauwa S Garba

Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Hauwa S. Garba wacce aka fi sani da 'Mama' tana daya daga cikin wanda tauraruwar su ke haskawa a 'yan wasan Hausa a yanzu.

A zantawar da manema labarai suka yi da ita, yarinyar 'yar shekara 19, kuma haifaffiyar jihar Legas, ta bayyana irin abubuwan da suka ja ra'ayinta ta shiga harkar fim din Hausa.

'Yar wasan ta bayyana yanda ta tsinci rayuwar ta cikin shirin fim din Hausa. Tace ta tsinci kanta a cikin shirin fim din Hausa ne a lokacin da ta hadu da shahararren mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu Rarara. Ta ce kafin ta hadu da Rarara, tana zaune da Aunty ta a jihar Kano.

Mu ma'abota kalon shirin fim din Hausa ne, ta dalilin haka naji wasan ya fara kwanta mini a rai, kuma naji ina sha'awar shiga harkar. Bazan manta ranar da muke hirar 'yan fim din Hausa da wata 'yar uwata, na fada mata cewar ina sha'awar shiga harkar fim. Sai take ce mini ai ta san Rarara, daga nan tayi minijagora zuwa wurin shi.

Da muka hadu dashi sai yake fada mini cewar shi baya shirin fim, amma zai hada ni da wani wanda ya sani. Ba a dade ba ya hadani da shahararren mai shirya fina-finan Hausan nan Usman Mu'azu. TO tun daga nan na fara fitowa a shirin fim din Hausa.

Daga: Jaridar Aminiya

11 Aug 2018

[Audio] Rarara - Kowa Ya Fita Barawo Ne


Rarara Ya Chachaki Bukola Da Tambuwal Da kwankwaso.

Sabuwa waka da rarara ya rera wanda yake furta cewa "kowa ya fita barawo ne" umma ta gaida aisha.

Wanda kusan cewa wazirinsa yayi waka "Allah raka taki Gona" bugun lamba ne ka saurari wannan waka zaku dalilin fitar su domin gudun buhari.

Kada ka bari a baka labari ka saukar da wannan waka a wayoyinku.

Rarara- Kowa Ya Fita Barawo Ne