29 Jan 2018

Yanda ake mallakar miji

 JA'AFAR MAHMOUD ADAM
(Fitowa na (001)
Ku sani cewa ita rayuwa ta auratayya,
rayuwa ce wadda take ibada, wani fanni
ne mai zaman kansa wanda ake bukatar
ma'aurata su kasance sun kware a cikinsa,
domin su gudanar da shi bisa ga tsari.
Mu sani rayuwa ta auratayya babban
abin da ta ke ginuwa akan sa ita ce
"SOYAYYA". Da dai shari'a ba ta yadda ayi
aure ba bisa ga tilas, a shari'a ba tilasta wa
namiji ko mace don su auri juna, sai dai aja
hankalinta ko hankalinsa har ya yarda ko ta
yarda don ta aure shi ko ya aure ta.
Shi ya sa lokacin Annabi (S A W) da aka
daura auren wata budurwa sai taje wajen
Manzon Allah (S A W) cewa: gashi fa
iyayenta sun yi mata auren tilas, sai Annabi
(S A W) ya ce, mata kina da za6i, ko ki aure
shi, ko kuma kice ba ki yarda ba, dole a
sake ki".
Sai wannan yarinya ta ce: "Wallahi zan iya
hakuri zama da shi, amma abin da yasa
nayi wannan kara sai don iyaye su ji daga
bakinka cewa: basu da damar tilasta wa
"ya ta auri wanda ba ta so".
Wannan hadisi yana tabbata ce daga
bakin Manzon Allah ( S A W).
Kuma ku sani ita "Kauna" (Soyayya)
sakamakonta ne duniya ta ke zama lafiya.
Duk lokacin da aka nemi "Kauna" ko (Soyayya) aka rasa, to
sai a dinga samun
yawan fadace fadace da kuma yawan
tashin hankali.

9 Jan 2018

YADDA AKE HADA CAKE

INGREDIENTS:
•Flour rabin loka/mudu
•Butter simas 2
•Kwai 15
•Sugar gwangwani 2
•Baking powder cokali daya table spoon 
•Flavor quater tea spoon. 

PROCEDURE:
Ki sami kwano ko roba ki zuba Butter dinnan duka sai ki zuba Sugar, ki juya su ki yi ta buga shi domin Sugar din ya narke.

Daga nan sai ki zuba kwai ki yi ta buga shi sosai, idan kina da Mixer ma zai fi haduwa sosai. 

Sai ki zuba flour da baking powder da flavor ki yi ta bugawa, har sai kin ga ya hade. Wasu kuma suna zuba flavor da baking powder a flour kafin su juye.

Sai ki sami murfi ki rufe, ki je ki kunna oven, idan gwangwanin cake kike dashi sai ki shafa Butter ko Mai, idan kuma cup cake kike dashi to sai ki zuba kwabin ki sa a Oven ki gasa.

Note: Flavor na gari zaki yi amfani dashi, sannan idan kika cika domin kiyi gwaninta toh zayyi caccaki a saman cake din. 

Sannan Baking Powder din na gwangwani zaki yi amfani dashi, ba na roba ba, domin shine zai sa ya tashi sosai. 

Wannan shine the most simplest way na yin cake. Ki gwada dan kadan zaki ga canji. Ko baki sa milk ba zayyi dadi.

Idan zaki yi dan kadan kuma ga yawan da zaki sa abubuwa saboda kada ki yi dayawa yazo bayyi kyau ba ki yi asaran kaya

YANDA AKE WAINAR MADARA MAI DADIN GASKE

Ita dai wannan masar ana iya cinta da miyar
kabeji ko Alayyaho kuma zaki iya cinta haka,
Abubuwan Da Ake Bukata
1= Farar Shinkafa
2= Madara gari
3= yeas
4= Bakar hoda
5= Kwakwa
6= Gishiri
7= sugar
8= fulebo na Kwakwa
9= Ruwan kwakwa
Da Farko Saiki jika farar shinkafan ki ta
kwana, sai ki nika ta washe gari.
bayan kin nika shinkafar ki sai ki zuba yis
sai ki saka shi a rana ya yi kamar awa biyu.
Sannan sai ki dauko shi ki zuba ruwan
kwakwa kisa ki kawo madarar garin ki saka
sai ki kawo suger kisa sai ki kawo Bakar hoda kisa sai ki juya ya juyu sosai.
Shikenan Saiki Dauko Kaskonki Ki Fara Suya .

YANDA AKE FANKASAU


FANKASAU

1. Alkama rabin loka
2. Yeast tea spoon 1
3. Flour gwangwani 3
4. Mai


PROCEDURE: Farko zaki kai alkama a niqa miki sai ki tankade da rariyan
laushi shima flour a tankade shi a ciki.
Sai ki zuba ruwa kiyi ta juyawa har sai ya hade sosai. Kwabin kamar na fanke amma yafi fanke tauri sosai.
Sai ki rufe a barshi ya tashi sosai. Idan da daddare ne zaki soya da safe kina tashi kamar saura hour ďaya ki soya sai ki buga shi sosai da sosai. Idan kin ji akwai tsami zaki iya dan zuba ruwan kanwa ki buga. Sai ki rufe lokacin da zaki soya zaki ga ya sake tasowa sosai.
Sai a saka mai a wuta in yayi zafi sai a rinqa debo kwabin ayi fadi dashi ayi huji a tsakiya sannan a saka a mai ya soyu. In so samune a mata miyan ganye a zuba man shanu a kai shi
zuwa bakin salati. Ga sauki ga dadi.
Please don't mind my pictures ina da shan miya.
Note: Ana yin zallan kwabin da ruwan tsamiya amma ya kan sashi qarfi da tsami. Wani kuma zaki ga baya yi sai kaďan sai ki sa kanwa don ya kashe tsamin. Sannan koda baki cin fankasau kamar ni idan kina yin na flour nan tsaf zaki ci.
Zaki iya jiqa yeast ďin da ruwan dumi musamman idan a ranar zaki yi.
Fankasau akwai sauqi a yiwa maigida a canza baki. Ba a cika flour don zai sha miki mai kuma ba zayyi taushi ba. Idan na zallan alkama ne duka kwabin ďaya ne.

Daga 
@Aisha muhammad,
munagodiya

8 Jan 2018

YADDA ZA A MAGANCE KURAJEN FUSKA CIKIN SAUKI

urajen fuska ko pimples a turance wasu kuraje ne da suka fi fitowa a fuska musamman idan mutum yana ta’ammali da mayuka iri-iri ba tare da kula da man daya dace da fatar fuskar ba. 
Matsalar kurajen fuska tafi shafar Mata musamman matasa inda za’a ga wasu matan har nikab suke sanyawa a fuskokin Su saboda kar aga ta’adin da kurajen suka Yi musu a fuska.
Maza ma sukan fuskanci irin wannan matsala ta kuraje a fuska sosai.
Kadan daga cikin Abubuwan dake janyo kurajen fuska sun hada da:- 


(1) yawan cin Abu Mai maiko. 
(2) Amfani da mayukan da Basu dace da fatar fuska ba 
(3) Kwayoyin cuta 
(4) Shiga rana sosai 

Mutane da dama kan kashe makudan kudade don sayan maganin da zai magance musu kurajen amma kuma yawanci ba’a samun biyan bukata. Ana iya magance kurahen fuska ta wadannan hanyoyin : 


(1) Bawon lemon zaki:
Ana shafa bawon lemon zaki a inda abin ya shafa Sai a barshi ya kwana da safe Sai a wanke da ruwan dumi.

(2) Zuma:
Ana samun zuma Mai kyau a goga da auduga a fuska, a barshi zuwa Yan mintuna Sai a wanke. Za’a iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen Su fita.

(3) Ruwan lemon tsami:-
Ruwan lemon tsami wata sahihiyar hanya ce mai matukar amfani wajen maganin kurajen fuska. Lemon tsami yana taka rawar gani sosai wajen kashe kananan kwayoyin cuta a fuska da kuma fitar da maikon fuska. Yadda za’ayi amfani da lemon tsami shi ne a samu lemon tsami a matse ruwansa sai a samu auduga mai tsafta a dinga goge fuska dashi kafin a kwanta bacci, da safe sai a wanke fuskar da ruwan dumin. Za’a iya maimaitawa sau biyu ko uku a rana har kurajen su fita.

(4) Ganyen darbejiya / Man darbejiya
Ana kwaba ganyen darbejiya da man darbejiya a shafa a fuska zuwa mintuna biyar sai a wanke da ruwan dumi ko a dinga shafa man darbejiya da auduga a fuskar har zuwa lokacin da kurajen zasu baje. Kurajen fuska dai sun dade suna batawa mutane fuskokin su har ta kai wasu ma sun gaji da nemawa kansu magani, mata ma kan yi duk yadda zasuyi su rufe fuskokin su don kar a ga kurajen,wasu ma kanyi amfani da hodar foundation akai akai don boye kurajen dake fuskar su. Wannan hanyoyi da na lissafa da karin wasu zasu taimaka sosai wajen cire kurajen fuska cikin sauki ba sai mutum ya kashe makudan kudade ba wajen neman magani ba.